An sabunta: 6 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 16:53 GMT

Taron Gagarabadau na BBC

Garmaho

Fasahar intanet fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duniya gaba daya, har ta kai wasu na cewa sun fara manatawa da ko yaya rayuwa take kafin zuwan Intanet.

Hakan ya sa, gidan radiyon BBC mai watsa shirye shiryensa ga kasashen duniya ya shirya taro kan tasirin da intanet ke yi a kan rayuwar al'umma.

An kuma gudanar da taron ne a dakin taro na Shoreditch hall dake birnin London. Mutane masu magana da yarurruka daban daban sun gudanar da tattaunawa a wajen taron.

Bidiyon abubuwan da suka wakana a taron

An kuma watsa shirin ne kai tsaye ta tashoshin BBC na talbijin, da Radiyo da kuma ta shafukan intanet.

Tasirin intanet kan rayuwar Hausawa

Wakilin BBC, Bashir Sa'ad Abdullahi, ya halarci zauren taron na Shoreditch inda ya gabatar da wani bangare na shirin rana na sashen Hausa na BBC.

Ya kuma tattauna da baki biyu da su ma suka halarci zauren wato Farfesa Ahmed Amfani na jami'ar London, da kuma Mallam Ibrahim Fagge shi ma dalibi a jami'ar London.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.