An sabunta: 7 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 12:23 GMT

Zanga zangar kasar Girka

 • Zanga zangar Greece
  Tashin hankali ya barke a Athens babban birnin kasar girka a lokacin da dubban mutane suka bazama kan tituna don nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.
 • Zanga zangar Greece
  Taho mu gama tsakanin masu zanga zanga da 'yan sanda ta auku ne a lokacin wani yajin aikin gama gari da ya tsayar da al'amura cik a kasar.
 • Zanga zangar Greece
  Masu zanga zanga sun yi amfani da duwatu, da bam din da aka hada man fetur wajen kai hare-hare a kan 'yan sanda.
 • Zanga zangar Greece
  Wasu masu zanga-zangar sun yi yunkuri afka wa majalisar dokokin kasar, amma 'yan sandar kwantar da tarzoma sun kora su baya.
 • Zanga zangar Greece
  'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen kora masu zanga zangar yayin da suka durfafo ginin.
 • Zanga zangar Greece
  An dai gudanar da jerin gwano a sauran biranen kasar ta Girka, kamar wannan da aka gudanar a garin Thessaloniki, yayinda ma'akatan gwamnati suka bayyana fushinsu da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.
 • Zanga zangar Greece
  zanga zangar dai ta zo ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da yajin aiki na uku a cikin watanni, abin da ya janyo dakatar da zirga zirgar ababen hawa.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.