An sabunta: 18 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 13:59 GMT

Tabarbarewar hakar illimi a Maiduguri

Tabarbarewar hakar illimi a Maidugurin Najeriya

 • Makarantar Wulari
  A jihohin arewacin Najeriya ne aka fi samun koma baya wajen batun ilmin duk da kuwa rattaba hannun da gwamnatin tarayya tayi kan sabon tsarin nan na bayar da ilmi bai daya wato UBE.
 • Makarantar Wulari
  Tabarbarewar ilmin musamman na firamare ba wai ga karkara ya tsaya ba har ma da manyan biranen jihohin duk da kuwa irin makudan kudaden da gwamnatocin ke ikirarin kashewa a fannin ilmin
 • Makarantar Wulari
  Tabarbarewar ilimin da lalacewar makarantun firamare a jihohin Najeriyar abu ne da aka dade ana dangantawa da irin rikon sakainar kashi da mahukantan ke yi.
 • Makarantar Wulari
  Makarantar Firamare ta Wulari dake Maiduguri na daya daga cikin makarantun da a akwai bishiyoyi da yawa kuma an jingina musu alluna, yara na zaune a kasa malamai akan bencina.
 • Makarantar Wulari
  Akasari dakunan karatun sun zama kango,yara suna karatu ne a karkashin bishiya a yayin da suka mayar da kangon azuzuwan wajen wasannin tamoulla.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.