An sabunta: 19 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 14:47 GMT

Gumurzun 'yan adawa da sojoji a Thailand

Gumurzun 'yan adawa da sojoji a Thailand

 • Rikicin kin jin gwamnati
  Masu aikin agaji na daukar 'yan adawar da suka samu rauni zuwa asibiti, sakamakon tawomugama tsakanin masu jajayen kaya wadanda ke zanaga zanga da kuma sojojin Thailand a ranar 9 ga watan Mayu.
 • Rikicin kin jin gwamnati
  Ma'aikatan birnin Bangkok kawar da damarar masu zanga zangar adawa da gwamnati, bayan da hayaki ya turnuke birnin sakamakon cinnawa wani gini wuta da masu zanga zangar suka yi.
 • Rikicin kin jin gwamnati
  Sojojin Thailand na kokarin kawar da shingayen da masu zanga zangar adawa da gwamnati suka kafa, lokacin da suke tawo mugama da sojoji a Bangkok babban birnin kasar.
 • Rikicin kin jin gwamnati
  Jerin gawarwakin masu zanga zangar adawa da gwamnati akan tituna, ranar Laraba, 19 ga watan Mayu, a Bangkok, babban birnin Thailand.
 • Rikicin kin jin gwamnati
  Wani sojan gwamnatin Thailand da aka jiwa rauni bayan wata taho mugama da masu zanga zangar nuna adawa da gwamnati a Bangkok.
 • Rikicin kin jin gwamnati
  Wasu daga cikin masu zanga zangar da sojoji ke tsare da su bayan da suka kama su a sansanin su dake Bangkok babban birnin kasar Thailand.
 • Rikicin kin jin gwamnati
  Hayaki ya turnuke sararin samaniyar Bangkok, babban birnin Thailand, bayan da sojoji suka kaddamar da farmaki kan sansanin masu zanga zanga.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.