An sabunta: 10 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 22:55 GMT

Hotunan Ku Masu Sauraro

 • Shagalin Sallah a Lagos
  Wani bangare na mahalarta walimar sallah ta 'yan jarida masu karbar horo a FRCN Training School, Ikeja, Lagos. Mai sauraronmu Ahmed Salisu ne ya aiko mana da hotunan.
 • Shagalin Sallah a Lagos
  Nan daya daga cikin mahalarta walimar sallah ta 'yan jarida masu karbar horo a FRCN Training School, Ikeja, Lagos kenan yake gabzar nama.
 • Shagalin Sallah a Lagos
  Nan kuma mai sauraronmu Ahmad Salisu wanda ya aiko mana da hotunan ne yake gyara bakinsa da kayan marmari bayan ya cika cikinsa da abinci.
 • Shagalin Sallah a Lagos
  Mahalarta walimar sallah ta 'yan jarida masu karbar horo a FRCN Training School, Ikeja, Lagos. Ahmed Salisu ne ya aiko mana da hoton.
 • Sallar Idi a Malyasia
  Nan wasu Hausawa mazauna kasar Malaysia ne a Masallacin Putra Jaya inda suka yi sallar Idi. Mai sauraronmu Muzakkir Mas'ud ne ya aiko mana da hotunan.
 • Sallar Idi a Malysai
  Nan ma wasu Hausawa mazauna kasar Malaysia ne a Masallacin Putra Jaya inda suka yi sallar Idi. Mai sauraronmu Muzakkir Mas'ud ne ya aiko mana da hotunan.
 • Sallar Idi
  Wani mai sauraronmu da bai rubuta sunansa ko inda ya aiko da hoton ba ya ke cewa an tsayar da sallah amma saboda gwamna ya makara wai dole sai an jira shi.
 • Shan ruwa
  Wani mai sauraren mu wato Ibrahim ne ya aiko mana da wannan hoton. Ya ce yana shan ruwa ne tare da abokinsa.
 • Belguim
  Gayyatar iftar da 'yan kabilar Pakistan su ka yi a daya daga cikin masalallcin su da ke birnin Antwerp a yankin Flanders ta kasar Belgium. Dakin dafa abinci kenan daidai lokacin da aka ji kiran sallah. Mohammed Ahmed India ne ya aiko mana hoton.
 • Belguim
  Kafin mu ci wannan abincin wato murgi aur alloo hade da biredin roti ko kuma chapatti,sai da mu ka bude baki da dabino,lemon kwali,strawberry,samosa da shayi mai kanshin citta.. Hoto daga Mohammed Ahmed India
 • Ambaliyar ruwa
  Daya daga cikin matsalolin dake ciwa al'ummar yankin Unguwar Dogon Zare Area tuwo a ƙwarya, musamman ma mazauna daura da titin Maiduguri shine malalar da ruwa keyi a duk san da aka yi ruwan sama, wanda hakan kan jefa al'ummar wannan yanki cikin halin ƙunci. Hoto daga Ahmad A. Umar
 • Tashe
  Mai sauraren mu Affan Buba Abuya ne ya aiko mana hotun wannan bawan Allah me shekara 34 da haihuwa ya na tashe a garin Gombe.
 • Tashe
  Mai sauraren mu Affan Buba Abuya ne ya aiko mana hotun wannan bawan Allah me shekara 34 da haihuwa ya na tashe a garin Gombe.
 • Tashe
  Mai sauraren mu Affan Buba Abuya ne ya aiko mana hotun wannan bawan Allah me shekara 34 da haihuwa ya na tashe a garin Gombe.
 • Tashe
  Mai sauraren mu Affan Buba Abuya ne ya aiko mana hotun wannan bawan Allah me shekara 34 da haihuwa ya na tashe a garin Gombe.
 • Faisal Ashiru Dan Liman
  Mai sauraron mu Faisal Ashiru Dan Liman a lokacin da yake bude baki a makarata a Malaysia. Ya ce ya yi buda baki da makaroni da limo da kuma ruwa.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Taron shan ruwa a Kebbi
  Taron shan ruwa na Kanawa da 'yan Jigawa mazauna jihar Kebbi a Najeriya. Abdulkadir Sardaunan Facebook ne ya aiko mana da hotunan.
 • Hotunan zaben cike gurbi a jihar Gombe
  Wannan hoton zaben cike gurbi ne da aka gudanar a jihar Gombe. Mai sauraren mu, manji aman854life@yahoo.com ne ya turo mana hoton
 • Hotunan zaben cike gurbi a jihar Gombe
  Wannan hoton zaben cike gurbi ne da aka gudanar a jihar Gombe. Mai sauraren mu, manji ya turo mana hoton.
 • Hotunan yadda mai saurarnmu Sanusi Isufu Aweisu yake shan ruwa
  Wannan hoton kayan abincin da mai sauraranmu Sanusi Isufu Aweisu ya sha ruwa da su kenan ranar azumi na 4 kamar yadda ya aikomana. Kayan sun hada da dabino da lemon zaki da gwandar masar da sauransu.
 • Hoton bude baki da wani mai sauraro ya aikomana
  Wannan shi ne yadda mai sauraranmu wanda bai rubuta sunansa ba, sai adreshinsa na email danejo02@yahoo.com, ya ke bude baki tare da 'yan uwansa kamar yadda ya aikomana a wannan hoton lokacin da yake shan ruwan.
 • Bikin cikar tsibirin Bermuda shekaru 400
  Wannan ita ce kofar shiga tsibrin Bermuda wanda ke karkashin Ingila daga filin jirgin sama. Mai sauraranmu Lawal Kaura ne ya dauko mana hotunan.
 • Bikin cikar tsibirin Bermuda shekaru 400
  An gudanar da bukukuwan cika shekaru 400 da kafuwar tsibirin na Bermuda mai yawan mutane akalla dubu sittin da bakwai (67,000).
 • Bikin cikar tsibirin Bermuda shekaru 400
  Kungiyoyi da dama sun nuna bajinta a wajen bikin, kamar yadda wadannan 'yan rawar na kungiyar Gombe suka taka a lokacin bikin na cika shekaru 400 da kafuwar tsibirin.
 • Daliban sashin koyon aikin jarida na makarantar kimiyya da fasaha ta Sokoto Polytechnic
  Daliban sashin koyon aikin jarida na makarantar kimiyya da fasaha ta Sokoto Polytechnic, lokacin da suka kawo ziyara ofishin sashin Hausa na BBC a Abuja, ranar 27 ga watan Yuli, 2010.
 • Daliban sashin koyon aikin jarida na makarantar kimiyya da fasaha ta Sokoto Polytechnics
  Daliban sun samu tarba ta musamman daga ma'aikatan BBC, inda aka yi musu bayanai kan yadda aikin jarida ke gudana a zamanance. Shugaban sashin Hausa na BBC Hajiya Jamilah Tangaza ta sawa daliban albarka.
 • Daliban sashin koyon aikin jarida na makarantar kimiyya da fasaha ta Sokoto Polytechnics
  A karshe daya daga cikin ma'aikatan BBC Abuja, Jimeh Saleh, ya gabatar da kyautar na'urar kwamfiyuta biyu ga daliban a madadin sashin Hausa na BBC, domin su bunkasa harkar karatunsu.
 • Hoton da mai sauraran mu Suleiman Aliyu Sabon Birnin Gobir yana bude baki
  Hoton da mai sauraran mu Suleiman Aliyu Sabon Birnin Gobir Sokoto, ya aikomana lokacin da yake bude baki da dabino da salat da farfesun naman rago da lemun kwalba bayan ya kai azumi.
 • Hoton mai saurarnmu Alasan Muhammad yana bude baki da iyalansa
  Hoton da mai sauraranmu Alasan Muhammad Dambatta ya aikomana lokacin da yake bude baki tare da iyalansa, bayan sun kammala azumin farko a birnin Makkah mai tsarki na kasar Saudiyya.
 • Nasarar kasar Spain a gasar cin kofin duniya
  Daruruwan 'yan kallo kenan a gindin babban allon talabijin a babbar kasuwar birnin ANTWERP na kasar Belgium, suna kallon wasan karshe na gasar cin kofin duniya tsakanin kasar Holland da Spain. Muhammad Ahmad Indiya ne ya aiko mana da hoton.
 • Nasarar kasar Spain a gasar cin kofin duniya
  Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain kenan suke cashewa bayan alkalin wasa ya hura usur suna da ci daya mai ban haushi a kan kasar Holland. Muhammad Ahmad Indiya ne ya aiko mana da hoton.
 • Abin da wannan bawan Allahn dan kasar Spain ke nufi da ya ware yatsu biyu bayan an tashi daga wasa inda kasarsu ta samu nasara shi ne, ai mu ne zakarun turai da kuma duniya baki daya a kwallon kafa. Muhammad Ahmad Indiya ne ya aiko mana da hoton.
 • Nasarar kasar Spain a gasar cin kofin duniya
  Duk da cewar Litinin rana ce ta aiki, amma a wajen wadannan 'yan kasar Spain din kamar yanzu aka fara yin dabdala bayan kasar su ta samu nasarar zama zakarar duniya. Muhammad Ahmad Indiya ne ya aiko mana da hoton.
 • Magoya bayan kasar Holland
  Magoya bayan kasar Holland kenan suna murna a Irish sports cafe da ke birnin Antwerp na kasar Belgium bayan sun samu kaiwa ga wasan karshe a gasar cin kofin duniya. Muhammad Ahmad Indiya ne ya aiko mana da hoton.
 • Shugaban Turkiyya Abdulla Gul
  Shugaban kasar Turkiyya Abdulla Gul yana jawabi, a lokacin ziyarar da ya kai Najeriya. BM Bashir ne ya aiko mana da hoton
 • Shugaban Turkiyya
  Shugaban na Turkiyya ya je Najeriyar ne domin halartar taron kasashe takwas masu tasowa wadanda ke da dimbin al'ummar Musulmi wato D8. BM Bashir ne ya aiko mana da hoton
 • Shugaban Turkiyya Abdulla Gul
  A lokacin taron nasu shugabannin sun maida hankali ne ga batutuwan da suka hada da kara yawan kasuwanci tsakaninsu zuwa dala tiriliyan 1.7 nan da shekara ta 2012.
 • Ziyarar shugaban Turkiyya Abdulla Gul
  Shugaba Abdulla, ya kuma ziyarci makarantar nan ta Nigerian Turkish International College wadda wasu 'yan kasar Turkiyya suka kafa a Abuja. BM Bashir ne ya aiko mana da hoton
 • Ziyarar shugaban Turkiyya Abdulla Gul
  Harabar makarantar Nigerian Turkish International College da shugaban Turkiyya ya ziyarta. BM Bashir ne ya aiko mana dahoton.
 • Yara a cikin kwata
  Ya kamata iyaye su rinka kulawa da 'ya`yansu ta hanyar sanin daga ina suke, kuma ina za su, Saboda tarbiyya. Pharm Salisu Hashim Muhammad ne ya aiko mana da wannan hoton
 • Hadarin mota a Abuja
  Wannan wani hadarin mota ne da ya faru a ranar 10 ga watan Mayu 2010, akan hanyar zuwa Kubwa daga cikin birnin Abuja, Najeriya. Ba wanda ya rasa rayuwar sa a lokacin da abun ya faru amma wadansu sun ji rauni sosai. Murtala Abdullahi ne ya aiko mana da hoton.
 • Yaro dauke da kaya
  Wannan hoton wani karamin yaro ne dauke da kayan itace da ya yiwo zai kai wa malaminsu. Anya kuwa almajiranci ba ya cikin abin da ake cewa bautar da yara, ko ci da gumin yara wato child abuse a turance? Hamisu Gumel ne ya aiko da hoton.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.