An sabunta: 24 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 13:56 GMT

Wasan Dambe na ci gaba da tasiri a Afrika

 • Wasan dambe
  Wasan dambe, wasa ne da aka dade ana yinsa a sassa da dama musamman a arewacin Najeriya,
 • Wasan dambe
  Ana karawa ne tsakanin mutane biyu, wadanda kowanne su ke kokarin gamawa da dan uwansa ta.
 • Wasan dambe
  Da zarar an kaiwa wani hari, nan da nan sai 'yan kallo su rude da ihu. Duk wanda ya kwantar da dan'uwansa to shi ne ya samu nasara.
 • Wasan dambe
  A kan kammala gasar a zagaye uku, amma idan wasa yayi wasa akan shafe sa'a guda ana gwabzawa,
 • Wasan dambe
  Kafin fara gasar dai 'yan damben kan shirya kansu sosai, domin kara irin tasirin da za su iya yi.
 • Wasan dambe
  'Yan damben kan rabu zuwa kungiyoyi daban daban inda suke karawa da juna, a mafi yawan lokuta.
 • Wasan dambe
  Muhammad Sani wani Bafulatani ne, kuma ya ce "ya taba kashe wani a dambe. amma yana saran za a dau fansa".
 • Wasan dambe
  A wannan karawar Muhammad ya sha kashi a hannun Shagon Dantagaye, abinda ya kawo karshen adawar da suka dade suna yi.
 • Wasan dambe
  'Yan damben kan yi amfani da kwayoyi kamar tabar wiwi domin kara kuzari a fagen daga.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.