An sabunta: 25 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 21:32 GMT

Ya kamata Najeriya ta fadada hanyoyin samun kudadenta - In Ji Jonathan

 • Shugaban Najeriya na kaddamar da masana'antar sarrafa ma'adinai
  Shugaban Nijeria, Dr Goodluck Jonathan ya jagoranci bikin bude wata masana'antar sarrafa ma'adinai a jahar Zamfara, inda ya ce ya kamata kasar ta fadada hanyoyin samun kudadenta.
 • raye-rayen gargajiya
  Shugaban dai ya kalli raye rayen gargajiya na manyan kabilun kasar da kuma na jahar da ya fito wato Bayelsa da suka zo yi masa maraba.
 • raye-rayen gargajiya
  Nan kuma wasu masu raye rayen gargajiya na kabilar Ibo, na yankin kudu maso gabashin Najeriya suke nuna irin tasu bajintar, a wajen bikin bude masana'antar sarrafa ma'adinai a Gusau jihar Zamfara.
 • raye-rayen gargajiya
  Su ma 'yan kabilar TiV daga jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya, ba a barsu a baya ba wajen nuna irin nasu raye-rayen na kabilar su.
 • raye-rayen gargajiya
  'Yan kabilar yarbawa daga yankin kudu maso yammacin Najeriya su ma sun baje kolin tasu kwarewar wajen raye rayen al'adun gargajiya. Haruna Shehu Tangaza ne ya dauko mana hotunan

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.