An sabunta: 15 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:28 GMT

Illar hakar mai ga muhalli a Najeriya

Illar hakar mai ga mahalli a Najeriya

 • Barazanar mai ga mahalli
  An shafe fiye da shekaru hamsin da biyu ke nan ana hakar danyen man fetur a yankin Niger Delta da ke kudancin Najeriya.
 • Barazanar mai ga mahall
  Saboda malalar mai a yankin, masu sana'ar kamun kifi a yankin na fuskantar kalubale da dama wajen tafiyar da sana'ar su.
 • Barazanar mai ga mahalli
  Yankin Neja-Delta a Najeriya ya dade yana jan hankalin kungiyoyin kare hakkin dan adam da masu fafutukar kare muhalli da masu neman adalci kan harkokin kasuwanci a duniya.
 • Barazanar mai ga mahalli
  Ana dai zargin manyan kamfanoni da suka hada da Shell da Chevron da Mobil da laifin cutar jama'ar yankin ta hanyar lalata musu muhalli sakamakon ayyukan hakar man.
 • Barazanar mai ga mahalli
  Wannan lamari na kara jan hankalin jama'a a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan malalar da mai ke yi a kogin Mexico na Amurka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.