Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga :Me ke janyo baiwa hamata iska a majalisun dokokin Najeriya?

A tsarin demokradiyya, ana zaben majalisun dokoki ne domin su kare bukatun jama'a.

Sai dai a wasu lokuta a kan yi zazzafar muhawarar da ke kaiwa ga ba hammata iska. Irin hakan na neman zama ruwan dare a majalisun dokokin Najeriya.

Ko da a wannan makon ma hakan ta faru a majalisar wakilan tarayyar Najeriya, inda har aka raunata wasu 'yan majalisar, tare kuma da yayyaga tufafin wasu.

To tambaya a nan ita ce, 'yan majalisar na kokarin sadaukar da kansu ne wajen kare bukatun jama'a? Ko kuma dai suna yi don kansu ne?

Irin abubuwan da filin Ra'ayi Riga na wannan mako ya duba kenan tare da wasu da abin ya shafa.

Daga cikinsu akwai Honourable Abba Anas Adamu, dan majalisar wakilan tarayya, na bangaren 'yan kungiyar The Progressives, wadanda suka nemi a tsige kakakin majalisar, Dimeji Bankole, har ta kai ga baiwa hammata iska.

Haka kuma akwai Honourable Sada Soli Jibiya dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya, mai goyon bayan kakakin majalisar.

Har ila yau, kuma daga cikin bakin akwai Awwal Musa Rafsanjani, na kungiyar CISLAC mai nazari a kan ayyukan majalisun dokoki a Najeriya sannann kuma akwai wasu daga cikin tarin masu sauraro da suka shiga cikin shirin ta wayar salula.