An sabunta: 8 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 15:58 GMT

Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya

Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya

 • Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya
  Daya daga cikin matsalolin zamantakewa da ake fama dasu arewacin Najeriya itace kaurar yara zuwa birane da suna neman ilmin addinnin musulunci inda bara ne babbar hanya samun abinci a garesu.
 • Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya
  Wasu lokutta dai irin wadannan yara sukan samu kawunansu cikin halin aikata miyagun laifukka a maimakon samun ilmin.
 • Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya
  Akan hakane wasu hukumomin a yankin arewa ke fitowa da hanyoyi daban daban domin shawo kan wannan matsalar.
 • Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya
  Makarantar gwaji ta Gwama ilmin Boko dana Addinin musulunci dake daf das hi ga birnin Sakkwato kenan da hukumomin jahar suka ce sun kafa da manufar rage kwararar almajiranda shekarunsu basu wuce na zuwa makaranta ba cikin birnin domin bara.
 • Makarantar tsugunar da almajirai a Sokoton Najeriya
  Wannan makarantar dai inji hukumomin ta gwaji ce kuma idan taci nasara za'a kakkafa ire-iren a sauran manyan hanyoyin shiga garin
 • Bayaga ilmin addinin musulunci an koyarda yaran darussan ,hausa,larabci lissafi dama turanci kuma ana ba yaran abinci a makarantar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.