Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Asusun hadin guiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomi: A dakatar ko a ci gaba?

A Najeriya, daya daga cikin batutuwan dake janyo kace-nace a sha'anin tafiyar da mulki tsakanin gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, shi ne tanadin tsarin mulkin kasar game da batun asusun hadin gwiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomin.

Kananan hukumomi dai su ne matakin mulki na uku, baya ga tarayya da jihohi, wadanda kuma jama'a ke ganin sun fi kusanci ga talakawa.

To sai dai korafin da wasu shugabannin wannan mataki na shugabanci ke yi shi ne cewar, tsarin da ake amfani da shi wajen rabon arzikin kasa, inda ake mika kasonsu ta hannun gwamnatocin jihohi na hana su sauke nauyin talakawansu game da alkawurran da suka yi musu a lokacin yakin neman zabe.

Su dai masu wannan korafi na cewa ne a rika ba su kasonsu kai tsaye, maimakon ta asusun hadin gwiwa da jihohi, domin tsarinda ake yanzu tamkar rijiya ta bada ruwa ne guga na hanawa.

A gefe daya, yayinda wasu ke cewa hakan na takura kananan hukumomin wajen gudanar da ayyukansu, wasu na cewar matakin ne ke tabbatar da ana sa ido kan yadda suke kashe kudade.

Shin ko ya dace kananan hukumomin su rika karbar kudadensu kai tsaye daga kwamitin rabon arzikin kasa na tarayya, ko kuwa a ci gaba da wannan tsari? Wadannan na daga cikin batutuwan da muka yi kokarin amsawa tare da ku masu sauraro, a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako.

Mun kuma gayyato baki da suka hadar da Dr Rabe Nasir, dan majalisar wakilai a Nijeriya, da Alhaji Dasuki Jalo Waziri, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi, ALGON, kuma shugaban karamar hukumar Gombe.

Akwai kuma Malam Muhammed Adamu, sakatare janar na kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta Nijeriya NULGE, da kuma Malam Abdulkarim Dayyabu, shugaban Rundunar Adalci.

Akwai kuma masu sauraro da suka bada tasu gudummawar ta wayar salula.

Za kuma ku iya ci gaba da muhawara a kan wannan batu a dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara, wato BBC Hausa Facebook.