An sabunta: 12 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 09:04 GMT

Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda

Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda

 • Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda
  Fiye da mutane sittin ne ake fargabar sun rasa rayukansu sakamakon tashin wasu bama-bamai guda biyu a Kampala, babban birnin kasar Uganda.
 • Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda
  Jami'an 'yansandan Ugandan sun dora alhakin fashewar da bama-baman a kan masu tayar da kayar baya na Somaliya. Sojojin kasar ne dai suka fi yawa a rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afirka, wadda ta ke ba gwamnatin Somaliya kariya.
 • Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda
  An tashi daya daga cikin bama-baman ne a wani mashahurin gidan cin abinci na Habashawa da ke unguwar Kabalagala a wajen garin Kampala, dayan kuma a wani kulob din wasan rugby da ke tsakiyar birnin.
 • Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda
  Tashin bama-baman kuma ya zo ne a daidai lokacin da ake wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya; kuma a wuraren da kan cika da 'yan kallo.
 • Bama-bamai sun hallaka jama'a da dama a Uganda
  A baya dai kungiyar ta al-Shabab, wadda ake zargin tana da alaka da Al Qa'ida, ta yi barazanar za ta kai hari a Kampala saboda goyon bayan da Uganda ke baiwa gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.