An sabunta: 20 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 12:43 GMT

Hotuna: Sa hannun Shugaba Goodluck a dokar zabe

Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe

 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  A Najeriya shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya sa hannu a kan dokokin zaben kasar. Ibrahim Isa ne ya dauko mana hotunan.
 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  An dauki wani lokaci ana sukar bangaren zartarwar da jan-kafa wajen rattaba hannun.
 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  Shugaban kasar dai ya sanya hannun ne a wata kwarya-kwaryar biki a ofishinsa.
 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  Kuma bikin ya samu halartar wakilin shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilan kasa.
 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  Shugaban Najeriyar ya ce wannan biki na sa hannun wata hujja ce, da za ta kawar da shakku daga zuciyar duk wani da ka iya kokwanton dukufar gwamnati wajen inganta harkar zabe a kasar.
 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  Har ma ya kara da cewa ba zai bari son zuciya ya hana masa yin duk wani abin da zai inganta harka zabe ba ko da kuwa yin hakan ba zai farantawa jam`iyyarsa ba.
 • Shugaba Goodluck Jonathan ya sa hanu a dokar zabe
  An yi ta zargin cewa shugaban kasar ya yi amaja ne saboda wasu sassan dokokin za su takaita wa shi kansa da sauran masu iko a kasar damar tankwara harkar zabe, musamman ma wajen sarrafa jam`iyyun siyasa.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.