An sabunta: 27 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 12:31 GMT

Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa

Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa

 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  Tashe wata al'adace a kasar Hausa da ake yinta yayinda azumi ya kai Goma har zuwa karshensa.
 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  Yara maza da mata wani lokacin ma har da matasa sun ke gudanar da wannan al'ada.
 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  Dare shine lokacin da aka fi gudanar da tashe, duk da cewa dai ana kuma gudanar da shi da rana.
 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  Masana dai sunce wannan al'ada mai dadadden tarihi ana gudanr da ita ne domin sanya nishadi a cikin zukatan jama'a.
 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  A mafi yawan lokuta, masu gudanr da tashe kan yi shiga ta musamman tare da shafa toka, ko hoda, ko bula a fuskarsu, wasu lokutan ma har sa fuska suke yi, sannan su hau kwararo kwararo suna kida kide da wake wake.
 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  A mafi yawan lokuta masu tashen su kan riga ambatar wata sana'a da suka yi suka yi kicibis da wani dake gudanar da ita, domin dai su ja hankalinsa ya dan basu imma dai kudi, ko kuma irin wannan abinda yake sayarwa.
 • Hotuna: Al'adar tashe a kasar Hausa
  Tamkar dai sauran al'amuran rayuwa da suke da shugabanni, shima tashe a Kano yana da shugaba, wanda sarkin Kano ya nada, kuma shine shugaban duk masu tashe.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.