An sabunta: 31 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 11:07 GMT

Sana'ar bugun kaya a kasar Hausa

Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya

 • Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya
  Bugun kaya na daga tsofaffin sanao'in Hausawa tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar Hausa. Yusuf Ibrahim Yakasai ne ya dauko mana hotunan.
 • Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya
  Bugun dai yana a matsayin guga kafin a shigowar dutsen guga.
 • Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya
  A wancen lokacin dai an fi buga kayan sarakuna da kuma na saki da kuma kayan sawa masu nauyi.
 • Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya
  A Najeriya, yanzu sana'ar ta bunkasa ta zama wacce zamani ke tafiya da ita, domin kuwa matasa da dama kan kai kayansu domin a buga, musaman wadanda aka yi wa rini.
 • Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya
  Su ma 'yan kasuwa kan kai shaddodi da Kamfala da aka runa domin sayarwa, inda a wasu lokutan har akan fitar da su kasashen ketare.
 • Sana'ar bugun kaya: Dutsen gugar gargajiya
  Wakilin BBC ya ziyarci Unguwar Marmara daya daga cikin unguwannin da suka shahara da sana'ar ta bugu a Kano shekaru aru aru.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.