An sabunta: 13 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 12:32 GMT

Taron Ministocin kasashen da kogin Kwara ya ratsa su

 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  A Najeriya, ministocin albarkatun ruwa na kasashen da kogin Kwara ya ratsa su, sun fara wani taro a kasar.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Taron dai sharar-fage ne ga babban taron da shugabannin kasashen za su yi a Najeriyar, a ranar Alhamis mai zuwa, kuma zai mai mai da hankali ne wajen tattaunawa a kan yadda kasashen za su inganta kogi don amfanin junansu ba tare da wani bangare ya cutu ba.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Wasu daga cikin kasashen dai na bayyana fargabar cewa ruwan kogin na ja da baya sakamakon rashin yasa da kuma madatsun ruwan da wasu takwarorinsu suka gina.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Taron, wanda hukumar raya kogin kwara ta shirya, shi ne karo na tara, kamar yadda mahalarta suka bayyana, kuma zai yi kokarin fayyace ire-iren kalubalen da al`umomin da kuma kasashen da kogin kwara ya ratsa ne ke fuskanta da nufin daukan matakan da suka dace don tunkurar kalubalen.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Wasu daga cikin matsalolin su ne yadda kasa da yashi da wasu abubuwa suka cike kogin suka rage masa zurfinsa, kuma hakan ya haddasa raguwar ruwan tare da kawo cikasga harkar sufuri ta cikin ruwan.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Wata matsalar kuma ita ce yadda kasashen za su sarrafa kogin wajen biyan bukatunsu daban-daban ba tare da wani bangare ya kuka ba.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Nigeriya na daga cikin kasashen da ke kukan cewa kokarin da wasu kasashen da ke cikin wannan tafiyar, cikinsu har da kasar Nijar ke yi na gina wasu madatsun ruwa don samar da da wutar lantarki da bai wa al`umominsu damar yin noman rani zai janyo raguwar ruwan da ke kwarara zuwa kasashen nasu.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Kuma zai yi illa ga harkokin da suke gudanarwa ta hanyar sarrafa ruwan kogin kwarar.
 • Taron kasashen da kogin Kwara ya ratsa su
  Amma ministan Albarkatun ruwan jamhuriyar Nijar Janar Abdu Kaza ya ce babu wani abin fargaba a cikin lamarin, saboda akwai matakai da kasashen nasu ke bi wajen gina madatsun ruwan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.