An sabunta: 11 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 12:58 GMT

Najeriya

Hotunan ku masu sauraro

Hotunan masu sauraro

 • Zanga-zanga a Kano
  Wasu mata da suka shiga sahun masu zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya. Mai sauraron BBC Aliyu Mukhtar Kwalli ne ya aiko mana da hoton.
 • Aikin Hajjin Bana
  Mai sauraren Sashen Hausa na BBC, Alasan Muhammad Dambatta, shi ne ya aiko mana da wannan hoton wanda ya dauka yayin aikin Hajjin Bana wato shekara ta 2011
 • Hotunan masu sauraro
  Wani mai sauraren Sashen Hausa na BBC, Buhari Haruna, shi ne ya aiko mana da wannan hoton, inda wani mutum ya shake wani dan sanda a Najeriya
 • Mai sauraron BBC Hafizu Balarabe Gusau
  Mai sauraron Sashen Hausa na BBC, Hafizu Balarabe Gusau, a jihar Zamfara, ya na zaune a shagonsa.
 • Mai sauraron BBC Bashir Mukhtar Yusuf
  Mai sauraron BBC Bashir Mukhtar Yusuf ( Big Bash) Unguwar Juma Zaria a jihar Kadunan Najeriya, yana dauke da rediyon da ya ke sauraron BBC da ita. Muna bukatar ku ma ku aiko mana da irin wadannan hotunan na ku, domin mu wallafa a shafinmu na bbchausa.com
 • Hotunan masu sauraro
  Jama'a sun taru suna kallon wutar da ta tashi bayan wata motar tanka ta yi hatsari a kan hanyar ta ta zuwa Gombe. Mutanen ukuin da ke cikin motar sun kone. Yakubu Yari Bawa ne ya aiko mana da hoton.
 • Hotunan masu sauraro
  Aikin tantance masu zabe a jihar Jigawa. Kamar yadda Mohd Suleman Hadejia ya aiko mana
 • Hotunan masu sauraro
  Yadda jama'a suka fito domin kada kuri'arsu kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya basu dama a jihar Sokoto. Bello BG Gidanmadi ne ya aiko mana da hoton
 • Hotunan masu sauraro
  Jami'an hukumar INEC na aikin tantance masu kada kuri'a a birnin Kanon Dabo, kamar yadda Abdurrahman Saleh ya aiko mana
 • Hotunan masu sauraro
  Aikin tantance masu kada kuri'a a unguwar APAPA da ke birnin Legas, inda mai saurarenmu Ubale ya aiko mana
 • Hotunan masu sauraro
  Yadda jama'a suka yi tururuwa a mazabar Unguwar Halilu, domin kada kuri'unsu a zaben 'yan Majalisun Tarayyar da aka dage. Aminu Iro ne ya aiko mana da hoton
 • Hotunan masu sauraro
  Ma'aikatan Hukumar zabe ta Najeriya INEC, na komawa hedikwatar su da ke Karamar Hukumar Bagwai bayan soke zaben 'yan Majalisu. Aliyu Umar ne ya aikoma da hoton
 • Hotunan masu sauraro
  Aikin gona na samar da hanyar kudin shiga ta fuskoki da dama.Tun daga sharar gona har zuwa girbi, dako da sarrafa amfanin gona. Jama'a mu rungumi aikin noma domin kauda talauci. Sule Sale ne ya aiko mana
 • Hotunan masu sauraro
  Jama'a sun taru suna murnar zagayowar ranar haihuwar ma'aiki Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam. Muhammad Yahya ne ya aiko mana da hoton
 • Hotunan masu sauraro
  Wani rakumin daji kenan a wani gandun daji na Nijar koure, wanda ke da nisan kilo mita 60 daga birnin Yamai. Rakuma kusan dari uku ne a wurin. Illiassou Bazo Dan Fulani ne ya aiko mana da hoton.
 • Hotunan masu sauraro
  Wasu yara da Majalisar Dinkin Duniya ta bawa horo domin sanin hakkinsu, bayan da aka yi amfani da su a matsayin sojoji ba tare da son ransu ba a Sudan. Hussaini Ali ne ya aiko mana da hoton.
 • Hotunan masu sauraro
  Wannan wata mota ce da ta kone a harin bom din da aka kai a birnin Alexandria na kasar Masar, mintina talatin da shigar sabuwar shekara ta 2011. Mutane da dama ne suka rasa rayukansu. Mamane Lawan Hassan ne ya aikomana da hoton.
 • Hotunan masu sauraro
  Damina ta yi albarka. Shikar shinkafa kan sa mace ta sami N30 a duk buhu da ta sheke. A kadada daya za a iya samun buhu 20, kenan mace za ta iya samun N600, a kan kowacce kadada a wuni. Sule Sale ne ya aiko mana da hoto
 • Hotunan masu sauraro
  Farashin dabbobi ya tashi a kasuwanni ganin yadda sallah ta karato, ga shi babu isassun kudade a hannun jama'a. Affan Buba Abuya ne ya aiko da wadannan hotuna daga Gombe
 • Hotunan masu sauraro
  Farashin dai ya kan ban-banta daga wuri zuwa wuri, amma kusan a ko'ina jama'a na korafin cewa farashin ya tashi, ga kuma karancin kudi.
 • Hotunan masu sauraro
  Hoton magoya bayan klob din Chelsea da Liverpool suna kallon karawar da suka yi a karshen makon da ya wuce a Kafin Madaki. Ubale Randi ne ya aiko mana da hoton.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.