An sabunta: 14 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 18:38 GMT

Ambaliyar ruwan Kebbi cikin hotuna

 • Kebbi Floods
  Hukumomin jahar Kebbi sun ce, akalla mutane dubu goma ne suka shiga gudun hijira, sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a karshen makon jiya.
 • Kebbi floods
  Wannan dai ya biyo bayan fashewar wata madatsar ruwa a makwabciyar jahar Sakkwato.
 • Kebbi Floods
  A cewar hukumomin, ruwan ya lalata dubban hectoci na shinkafa, da kuma gadoji akalla hudu.
 • Kebbi Floods
  Hakan na faruwa a daidai lokacin da kuma ake fargabar cewa, ruwan da ke cigaba da kwarara zuwa kuryar jahar ta Kebbi, zai iya jefa wasu dimbin mutanen cikin mawuyacin hali.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.