An sabunta: 21 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 13:16 GMT

Taron hukumar zabe da shugabannin jam'iyyun siyasa a Najeriya

  • A Najeriya, Hukumar zaben kasar na tattaunawa da shugabannin jam`iyyun siyasa don duba yiwuwar tura babban zaben kasar na badi daga watan Janairu zuwa gaba.
  • Hukumar zaben dai ta bayyana cewa da wuya ta iya gudanar da sahihin zabe ta hanyar amfani da jadawalin da ta fitar, sakamakon yadda aka tattakura al`amura.
  • A cewar hukumar, ko da za ta tura zaben gaba to ba zai shafi tsarin da aka yi na rantsar da shugaban kasa a watan Mayu mai zuwa ba.
  • Hukumar zaben Najeriyar, kamar yadda shugabanta, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana ta samu dukkan goyon bayan da take bukata daga gwamnati ta fuskar kudi don gudanar da babban zaben kasar na badi.
  • Sai dai bayan ta yi tsam ta duba yadda ta jera hidimomin da ke gabanta baki-da-hanci, ta fahinci cewa aka yiwuwar ayyukanta su dagule idan aka samu tangarda komai kankantarta.
  • Kuma wannan ne ya sanya hukumar ta nemi shugabannin jam`iyyu domin su tattauna da juna tare da ba da shawarwari ta yadda za a gudu-tare-a-tsira tare.
  • Sai dai jam`iyyun siyasa a nasu banagaren cewa suka yi wannan hanzari da na hukumar zabe bai ba su mamaki ba.
  • Binciken da na yi dai ya nuna cewa wasu jam`iyyun siyasar su ma za su amfana daga tura zaben zuwa gaba, saboda zai ba su damar kara kintsa wa zaben, musamman ma yadda wasunsu ke fama da rigingimu.
  • Har zuwa lokacin da nake hada wannan rahoton dai hukumar zaben ba a kai ga tsai da lokacin da ake ganin zai fi a`ala a gudanar da zaben ba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.