An sabunta: 26 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 17:08 GMT

Yakin Basasar Najeriya

Yakin Basasar Najeriya

 • Yakin Basasar Najeriya
  A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, turawan Ingila sun mika tutar 'yancin kan Najeriya ga Pira Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda dan arewa ne yayinda Dr. Nnamdi Azikiwe ke matsayin shugaban kasa.
 • Yakin Basasar Najeriya
  Tun daga wannan lakacin sauran kabilun musamman Ibo ba su ji dadin cewa 'dan arewa ne ke mulkarsu ba, kuma wannan ne ya haifar da juyin mulki na farko da sojoji yawancinsu 'yan kabilar Ibo suka yi a shekarar 1966 inda aka kashe manyan shugabannin Arewa.
 • Yakin Basasar Najeriya
  Kashe wadannan shugabanni da suka hada da Pira Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Pirimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, yasa a watan Yulin shekarar 1966, Laftanal Kanal Murtala Muhammed ya jagoranci wani juyin mulkin, wanda ya kawo Laftanal Kanal Yakubu Gowon a matsayin shugaban mulkin soja.
 • Yakin Basasar Najeriya
  Zargin nuna banbanci ga kabilar Ibo ya sa a lokacin gwamnan soji a kudu maso gabas Kanal Odumegwu Ojukwu ya nemi ballewar yankin daga Najeriya ranar 30 ga watan Mayun shekarar 1967 domin kafa kasar Biafra.
 • Yakin Basasar Najeriya
  Wannan shi ne mafarin yakin Biafra da aka kwashe kimanin shekaru uku ana yi a Najeriya, tsakanin 'yan kabilar Ibo dake neman kafa kasarsu da gwamnatin sojin wancan lokacin, karkashin shugabancin Laftanal Kanal Yakubu Gowon.
 • Yakin Basasar Najeriya
  A ranar 6 ga watan Yulin shekarar 1967 ne dakarun sojin Najeriya suka kutsa kai cikin yankin Biafran a kokarinsu na mamaye yankunan da suke neman kwacewa domin kafa tasu kasar.
 • Yakin Basasar Najeriya
  A ranar 13 ga watan Janairun shekarar 1970 ne, kwanaki bayan da Ojukwu ya yi gudun hijira zuwa kasar Cote' dIvoire ko Ivory Coast, mataimakinsa Philip Effiong ya yi saranda ga dakarun sojin gwamnati,

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.