An sabunta: 1 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 13:14 GMT

Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya

Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya

 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Akalla mutane goma ne suka mutu bayanda wasu bama-bamai suka tashi a kusa da wajen da ake bikin murnar cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Majiyar 'yansanda ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters faruwar abin. Inda ta kara da cewa mutane takwas sun mutu kawo yanzu, ciki har da jami'an 'yansanda.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Amma wani ma'aikacin hukumar kashe gobara ya shaidawa BBC cewa sun gano gawarwaki goma.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Bama-bamai biyu ne suka tashi wadanda suka lalata motoci uku, tare da jiwa wasu mutanen raunuka.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Sai dai an ci gaba da shagulgulan murnar ranar samun 'yancin kan kamar yadda aka tsara.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Harin ya zo ne mintuna kadan bayanda kungiyar MEND mai fafutukar kwato yankin Niger-Delta, ta yi gargadin cewa za ta kai hare-hare a wajen bikin samun 'yancin kan.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Editan BBC a Abuja Ahmed Idris ya ce ya ga kafafuwan mutane sun yi jina-jina a wurin da abin ya faru, yayinda ma'aikatan agaji ke kokarin sasu a motoci.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Kungiyar Mend tace jami'anta da ke aiki a cikin rundunar 'yan sandan kasar ne suka dasa bama-bamai a wasu motoci da ke wurare daban daban.
 • Bom ya kashe mutane da dama a Najeriya
  Wakilinmu ya kara da cewa akwai yiwuwar wani bom din na uku ya kara tashi a filin da ake taron. Da farko jami'an tsaro a wajen sun ce bindiga ce ta tashi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.