An sabunta: 1 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 03:42 GMT

Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50

Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50

 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  A ranar da Najeriya ta samu 'yancin kai yau shekaru hamsin da suka gabata, an gudanar da bukukuwa a duk fadin 'kasar a matsayinta na wata rana dake cike da dumbin tarihi ta fuskoki da dama.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  An gudanar da wasan wuta a cibiyar raya al'adu ta kasa da ke birnin Abuja domin murna da cikar Najeriya shekaru hamsin da samun 'yancin kai.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  Mawaka da makada daban daban ne daga fadin kasar suka cashe a wurin domin taya jama'a farin ciki.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  Wanann biki shi ne na maraba da irin shagulgulan da ake saran za su biyo baya domin maraba da wanann rana da Najeriya ta samu 'yancin kai daga Burtaniya.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  Bikin ya samu halartar shugaban kasar da sauran manyan jami'an gwamnati da kuma manyan baki daga ciki da wajen kasar.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  Wasu 'yan Najeriya da suka zanta da BBC a wajen bikin sun nuna farin cikinsu da ganin wanann rana, tare da yin fatan alheri ga kasar.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  Bikin tunawa da samun 'yancin kan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan halin rayuwar da jama'a ke ciki musamman ta fuskar tattalin arziki.
 • Bukukuwan cikar Najeriya shekaru 50
  Fatan 'yan kasar dai shi ne wannan ya zamo wata dama da mahukunta za su maida hankali wajen kawar da abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya ta fuskar tattalin arziki daci gaban rayuwa, ba wai kawai a kare a bukukuwa ba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.