An sabunta: 6 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 14:15 GMT

Hotunan mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast

Hotunan mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast

 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  An kafa wata rundunar mata zalla a birni mafi girma na kasar Ivory Coast a shekarar da ta gabata, domin kalubalantar ra'ayin wasu 'yan gargajiya dake ganin bai kamata mata su shiga aikin 'yan sanda ba.
 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  Rundunar matan su 318, wadanda shekarunsu ba su kai talatin ba, ana yi musu lakabin "Tagro's babes" ko "Tagrottes", wanda ya samo asali daga sunan ministan cikin gida Desire Tagro.
 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  Rundunar ita ce irinta ta farko ta mata da ake baiwa horaswa irin na 'yan sanda, sannan su kuma kara samun wani horon da zai taimaka musu wajen zirga-zirga tsakanin motoci.
 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  Sai dai rundunar 'yan sandan ta mata zalla na fuskantar matsala a yanzu, domin kusan kaso daya bisa hudu na ilahirinsu a yanzu na hutun da mata ke dauka don zuwa haihuwa.
 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  'Yan sanda matan, suna da cikakken ikon kama masu laifi, kuma suna dauke da kananan bindigogi, duk da cewa har yanzu ba su taba amfani da su ba, saboda suna samun taimako daga sauran jami'an tsaro.
 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  "Kodayaushe ina son habaka rawar da mata ke takawa a cikin al'umma" in ji Saja Irie Lou. "A wasu lokutan maza ba su son su karbi umarni daga mata, amma mun zo nan ne domin sauya hakan."
 • Mata masu baiwa motoci hannu a Ivory Coast
  "Ina farin cikin aiki tare da mata zalla, saboda mun fahimci junanmu," in ji Saja Coulibaly. Direbobi suna yaba wa da aikinmu. Kuma a lokuta da dama, mata na alfahari saboda irin aikin da 'yan uwansu ke yi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.