An sabunta: 1 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 15:59 GMT

Bikin gabatar da Samson Siasia

Bikin gabatar da Samson Siasia

 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  Hukumar kwalllon kafa ta Najeriya NFF, ta gabatar da sabon kocin Super Eagles Samson Siasia ga manema labarai a babban filin wasa da ke Abuja.
 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  Hukumar ta dau Samson Siasia ne na tsawon shekaru hudu, inda ta ce ta za ta kara tsawon wa'adin kwantiragin, idan kocin ya yi tasiri.
 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  Samson Siasia ya maye gurbin Lars Lagerback wanda ya ki sabunta kwantaragin sa da hukumar bayan an fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya da ta halarta a kasar Afrika ta kudu.
 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  Shugaban Hukumar NFF, Alhaji Aminu Maigari, ya ce hukumar za ta ba sabon kocin duk goyon bayan da yake bukata domin ya fitar da kasar daga kangin da take ciki.
 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  A hirar da ya yi da manema labarai jim kadan bayan gabatar da shi, sabon kocin Samson Siasia, ya yi alkawarin farantawa 'yan Najeriya rai ta hanyar inganta tawagar Super Eagles.
 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  Ya ce zai kafa wani sansani na musamman, domin horon 'yan wasan cikin gida a kasar, wanda ya ce, yana da kwarin gwiwa kasar na da 'yan wasan cikin gida da za su iya habaka tawagar ta Super Eagles.
 • Bikin gabatar da Samson Siasia
  Cikin wadanda suka halarci bikin dai har da mahaifan Samson Siasia.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.