An sabunta: 15 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 16:05 GMT

Nuhu Ribadu ya kaddamar da Kamfe

  • A Najeriya, tsohon shugaban Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati Malam Nuhu Ribadu, ya kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa, karkashin inuwar jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).
  • A jawabin da ya gabatar Malam Nuhu Ribadu ya yi Allah wadai da yadda al'amura ke tafiya a Najeriya a halin yanzu, inda ya ce wajibi ne 'yan kasar su ta shi tsaye domin kawo sauyi.
  • Babban abinda ya fi jan hankali a dogon jawabin da Malam Nuhu Ribadu ya shafe kusan mintina talatin yana karanta wa, shi ne alkawarin da ya dauka na kafa sabuwar Najeriya..
  • Malam Nuhu Ribadu ya kuma danganta halin da kasar ta samu kanta a ciki na koma baya da tsananin cin hanci da rashawa da ya dabai baye kowanne sashi na gwamnati.
  • Hajiya Naja'atu Muhammad na daga cikin 'yan siyasar da su ka gabatar da jawabi a wurin.
  • Masu lura da al'amura dai na ganin fitowar Nuhu Ribadu, za ta kara zafafa kokawar neman shugabancin kasar a jam'iyyar ta ACN, a daidai lokacin da jam'iyyar ke duba yiwuwar hada kai da wasu jam'iyyu domin duba yadda za su fuskanci zaben na badi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.