Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Rashin asibitoci a yankunan karkara

Image caption Mata na jiran ganin likita a asibiti

Masu iya magana dai na cewa lafiya uwar jiki babu mai fushi da ke, hakan ne yasa samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ke da matukar mahimmancin gaske, musamman wajen rage yawaitar mace-macen mata masu juna.

Kuma wannan alhaki ne da ake ganin ya rataya a wuyan hukumomi na samar asibitoci, dakunan shan magani, wadata asibitoci da kayayyakin aiki da kuma magunguna, bugu da kari samar da kwararrun likitoci da ma'aikatan jiyya da za su kula da mutane a wadannan asibitoci.

Sanin muhimmancin ingatanccen tsarin kiwon lafiya ne ga al'umma yasa a wasu kasashen duniya, musamman wadanda suka ci gaba ke ware kaso mai gwabi-gwabi na kasafin kudinsu don kashewa a fannin kiwon lafiya.

Kamar misali a shafin gwamnatin Burtaniya kan bayanai game da kudaden da kasar ke kashewa ya nuna cewa kasafin kudin Burtaniya na shekarar 2008 kuwa, kasar ta kashe kashi 18 cikin dari na kasafin kudin da ta a wannan shekara wato kusan Fan biliyan dari shida akan harkar kiwon lafiya.

Haka kuma a shekarar da ke biye da ita wato shekarar 2009 Burtaniya ta yi kasafin kudi da ya kai sama da fan biliyan dari shida, Burtaniya ta kashe kashi 17 cikin dari na wannan kudi akan harkar kiwon lafiya.

A shekarar 2010 ma cikin kasafin kudi da ya kai kimanin biliyan dari shida da hamsin, kasar ta kashe kashi 18 cikin dari kan harkar kiwon lafiya. Yayinda kasafin kudi na shekarar 2011 kuwa shima kasar zata kashe kashi 18 cikin dari na kasafin kudin da yakai kusan biliyan dari bakwai.

To itama Amurka dai a shekaru uku da suka gabata a jere daga shekarar 2008 zuwa 2010 ta kashe kashi 17 cikin dari na kasasfin kudin kasar ta ya kama daga dala biliyan dubu biyar zuwa sama da dala biliyan dubu shida, ne a kan fannin kiwon lafiya.

Hakan dai na kunshe ne a shafin yanar gizo dake nuna bayanai game da kudaden da gwamnatin Amurkan ke kashewa. Inda shafin kuma ya nuna cewa kason ya karu zuwa goma sha takwas na kasafin kudin kasar a shekarar 2011 wanda ya kai kusan dala biliyan dubu bakwai.

Ita kuwa kasar Najeriya wacce kusan ta ke bin tsari irin na Amurka, idan aka dubi kasafin kudin kasar na shekarar 2010 wanda ya kusan kaiwa trillion biyar, kasar ta ware kashi biyu da rabi ne cikin dari na kasafin ga fannin kiwon lafiya. Kuma cikin wannan kaso har da kudin albashin ma'aikata da kudaden alawus-alawus na tafiye tafiye.

Haka kuma wannan matsala dai ta taimaka wajen kawo komabaya a harkar kiwon lafiya a kasashe kamar su Najeriya. A yi sauraro lafiya.