An sabunta: 14 ga Janairu, 2011 - An wallafa a 02:48 GMT

Hotuna:Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP

 • A Najeriya, jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ta gudanar da babban taronta na kasa, inda wakilan jam`iyyar wato deleget-deleget za su kada kuri`ar fitar da mutumin da zai tsaya wa jam'iyyar takarar shugaban kasa.
 • Kafin a fara kada kuri'ar dai an gudanarda rawan al'adun gargajiya dana zamani domin nishadantar da manyan baki da kuma deleget din da su ka halarci dandanlin na Eagles Square.
 • Sai dai kuma an tsaurara matakan tsaro a dandalin na Eagles Square daga cikinta har waje, a yayinda jirgin sama mai saukan angula nata shawagi domin tabattar da tsaro.
 • Mutane ukun da jam`iyyar ta tantance su shiga takara sun sun hada da shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma Mrs. Sarah Jubril.
 • Deligate-Deligate din jihar Pilato, wanda suka hada da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Alhaji Ibrahim Mantu, da gwamnan jihar, Jonah Jang da kuma Cif Solomon Lar.
 • Sai wani mai sa-ido a kan zabe, Alhaji Salisu Yarima ya tabbatar wa da BBCa cewa wasu wakilan sun koka da tsarin zaben.
 • Deligate din jihar Gombe da gwamnan jihar, Alhaji Danjuma Goje ya jagoranta.
 • An dai fara kada kuri'ar ne a cikin dare bayan da yan takarar uku suka gabatar da jawabansu na neman kuri'u.
 • Jam`iyyar ta bi wani tsari ne na tanada wa kowace jiha akwatin kada kuri`a, inada aka dinga gayyatar jihohi daya-bayan-daya suna kada kuri`unsu.
 • Malaman zaben jam`iyyar Pdpn dai sun kashe dare wajen kidayar kuri`un da wakilai ko deleget-deleget suka kada a babban taron jam`iyyar.
 • Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya yi nasara da gagarumin rinjaye a kan abokan takararsa biyu, wato da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Mrs Sera Jibril.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.