An sabunta: 19 ga Janairu, 2011 - An wallafa a 13:12 GMT

Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya

 • Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya
  A ranar Asabar ne Hukumar zaben Najeriya ta fara aikin rijistar masu zabe a sassa daban-daban na kasar.
 • Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya
  Rahotanni sun nuna cewa 'yan kasar na fitowa sosai domin su yi rijistar, sai dai ana korafi kan tuntuben na'u'rori wanda ke haifar da jinkiri.
 • Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya
  Sai dai shugaban Hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya shaida wa BBC cewa a yanzu Hukumar ta shawo kan matsalolin.
 • Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya
  Kimanin 'yan Najeriya miliyan saba'in ne ake saran yi wa rijistar domin samun cancantar kada kuri'a a zabukan na watan Afrilu.
 • Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya
  Masana dai na ganin aikin rijistar wani zakaran gwajin dafi ne da ka iya nuna yadda zabukan kasar masu zuwa za su gudana.
 • Hotuna: Aikin rijistar masu zabe a Najeriya
  A baya dai an sha kokawa kan rijistar masu zaben, abin ya sa Hukumar zaben da ma jam'iyyun adawa su ka nemi a sake sabuwar rijistar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.