An sabunta: 8 ga Fabrairu, 2011 - An wallafa a 17:21 GMT

Hotuna: Taron gwamnonin arewa kan tsaro

  • A Najeriya, Kungiyar gwamnonin jihohin arewacin kasar ta gudanarda wani taro a Abuja domin duba hanyoyin da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka shafi tabarbarewar tsaro a jihohin Pilato da Bauchi da Borno.
  • Kungiyar dai ba ta yi wa manema labaru cikakken bayani a kan matakan da suka yi niyyar dauka ba, amma ta bayyana cewa za ta baiwa gwamnonin jihohi ukun cikakken goyon baya wajen shawo kan rikice-rikicen da suke fama da su.
  • Jihohin Pilato da Bauchi da Borno dai na fama da rigingimun addini irin su boko-haram, da na siyasa da kuma na kabilanci, wadanda ke ci gaba da yin sanadin mutuwar mutane da dama.
  • Kungiyar gwamnonin dai ta ce ta lura cewa masifar rikice-rikicen da jihohin Pilato da Borno da Bauchi ke fama da ita fitina ce wadda idan ba a shawo kanta ba, to ba za ta takaita ga iya jihohi ukun ba.
  • Kungiyar ta ce haka ne ya sa za ta kafa wani kwamiti mai mutum uku a zaman da ta yi a jihar Adama kwanan nan don ya yi nazarin matsalar tare da ba ta shawarwarin yadda za a magance ta, wadda kuma a zamanta na yau ne ta karbi rahoton kwamitin.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.