An sabunta: 2 ga Maris, 2011 - An wallafa a 17:02 GMT

Hotuna: Rikicin Libya

  • Sojojin Kanar Gaddafi na kai hare haren mayar da martani a yankin gabas da birnin Sirte dake tsakiyar kasar inda shugaba Gaddafi ya fi karfi.
  • Rahotanni sun ce dakarun dake biyayya da Kanar Gaddafin sun kai hari a kan birnin Al -Brayqa dake a yankin arewa maso gabacin kasar.
  • Rahotannin sun ce a halin yanzu dakarun Gwamnati ne ke iko da sararin samaniya da tashar jiragen ruwa na garin, sai dai masu hamayya sun ce an murkushe harin.
  • Ana dai sa ran cewa daga nan, dakarun Kanar Gaddafi za su mika zuwa garin Ajdabiya ta cikin rairayin hamada.
  • Sai dai 'yan tawayen da ke rike da garin sun musanta cewa dakarun sun sake kwace garin na al Brayqa.
  • Garin Ajdabiya dai na da babbar wurin ajiye makamai wadda dakarun na Gaddafi za su kaiwa hari.
  • A kwanaki goma sha biyun da suka gabata dai an yi yunkurin lalata wurin ajiye makaman ta hanyar jefa bama-bamai ta jiragen sama.
  • Yayin da ake ci gaba da ba-ta-kashi, a daya bangare kuma, an zargi Gaddafi da yin amfani da sojojin haya daga wasu kasashen Afirka ciki har da kasashen Mali, da Nijar, da Chadi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.