An sabunta: 14 ga Aprilu, 2011 - An wallafa a 11:55 GMT

Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja

Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja

 • Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja
  Rashin cikakkun hanyoyi da kaucewa ka'idojin tuki da kuma rashin hakuri na haifar da mummunan cunkoson motoci a manyan hanyoyin shiga birnin tarayyar Najeriya Abuja. Hotuna: Chris Ewokor.
 • Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja
  Wannan cunkoson kan haifar da cakudewar hanyar shiga ko fita daga Abuja ta wuraren Kubwa da Gwarinpa, inda jama'a kan shafe sa'o'i a hanyar.
 • Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja
  Lamarin ba a wannan bangare na birnin kawai ya tsaya ba, domin a sauran sassan shiga birnin ma lamarin haka ya ke - musamman ta bangaren Nyanya da Lugbe.
 • Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja
  Wani abu da ya kara zafafa lamarin shi ne na aikin gyaran hanyar ta Kubwa da ake yi, wanda aka shafe kusan shekara guda ana yi.
 • Hotuna: Cunkoson motoci a Abuja
  A duk lokacin da jama'a suka tashi daga aiki, ko kuma suke fitowa aiki, to hanyar na cushewa. Da dama daga cikin mazauna Abuja na zaune ne a wajen gari.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.