Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bob Marley: Shekaru 30 bayan rasuwarsa

Image caption Bob Marley

Dubban masoyan shahararren mawakin nan na Ragea, Bob Marley, sun gudanarda shagulgulan tunawa da mutuwarsa shekaru talatin da suka gabata.

Shi dai mawakin ya kasance mai farin jini a sassa daban-daban na duniya a lokacin da yake raye, da ma bayan mutuwarsa saboda abinda masoyansa suka kira kalmomi na karfafa gwiwa da kwato 'yancin wadanda aka danne, da yake amfani da su a cikin wakokin na sa.

Wakilin BBC Is'haq Khalid ya duba mana rayuwar Bob Marley, da kuma yadda masoyansa ke daukarsa a yayin da ake bukin zagayowar ranar mutuwarsa, kuma ya hada mana wannan rahoton.