An sabunta: 6 ga Yuni, 2011 - An wallafa a 12:59 GMT

Hotuna: Tokar aman dutse a Chile

  • An samu aman dutse a yankin Puyehue-Cordon-Caulle na kasar Chile, wanda kuma ya hadasa burbudin tokar da ta yi nisan muraba'in kilomita biyar.
  • An ranar Lahadi aman tokar wutar ta lullube sararin samaniya, inda ko'ina ya zama ja.
  • Wasu mazauna yankunan suna fargabar barin gidajensu, saboda gudun kada a sace musu kayayyakinsu da kuma dabbobi.
  • Aman dutsen ya shafi wasu bangarori na kasar Argentina dake makwabtaka da Chile. Wani dan sandan Argentina ne ya tsinto wannan dutsen.
  • Wasu na ganin aman dutsen kamar kusufin rana. Kuma sun ga kamar ana ruwan dusar kankara.
  • A garin Bariloche, wani wurin shakatawa a kasar Argentina, babu yiwuwar za a iya wasan golf a wurin saboda dusar kankara da ta lullube ko'ina.
  • Wasu motoci da tokar ta rufe. Mahukunta sun gargadi mazauna wurin da kada su shaki tokar. kuma sun rufe kofofin gidajensu.
  • Zancen ma haka ya ke a Puerto Madryn, a gabar tekun Argentina, tokar dai ta barbade ko'ina.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.