An sabunta: 23 ga Yuni, 2011 - An wallafa a 13:23 GMT

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Kano

Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Kano

 • Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Kano
  A kalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu, inda wasu da dama kuma suka jikkata, a unguwar Faggen da ke jihar Kano sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a ranar Talata.
 • Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Kano
  An shafe kimanin sa'a guda ana sheka ruwan saman a sassan jihar da dama. Kusan gidaje 30 ne suka ruguje sakamakon ruwan saman, kuma an yi hasarar dukiya mai yawa.
 • Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Kano
  Wasu shaidu sun ce fiye da shekara talatin kenan rabonsu da ganin ruwan sama irin wannan. Hotuna: Yusuf Yakasai
 • Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Kano
  Wannan matsalar ambaliyar dai ta zo ne a dai dai lokacin da masana ke wani taro a Abuja, a kan yadda za'a tunkari bala'in ambaliyar ruwa a kasashen yammacin Afrika.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.