An sabunta: 11 ga Yuli, 2011 - An wallafa a 12:31 GMT

Fari a kusurwar Afrika

Fari a Kusurwar Afrika

  • Mumunar farin na haddasa matsalar karancin abinci a kusurwar Afrika, wanda ke kunshe da kasashen Kenya da Habasha da Djibouti da kuma Somalia. Yanayi a yankin Pacific ya yi nuni da cewa an samu karancin ruwan sama a yankin na tsawon shekaru biyu, kuma a yanzu haka akwai yiwuwar ba za'a samu ruwan sama ba, sai a watan Satumba.

  • Karancin abinci ya shafi sama da mutane miliyan 12. Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana cewa ana fama da matsananciyar yunwa a wurare biyu a kudancin Sudan, a yayinda kashi 30 na yara a kasar na fama da ciwon tamowa, kuma yara hudu cikin dubu goma na mutuwa a kullum.

  • Ana ci gaba da samun kai agaji yankin ne saboda rikicin da ake fama da su a yankin, wanda kuma ke nufin cewa kungiyoyin masu fafutuka na hana kungiyoyin bada agaji shigowa kudancin Somalia da kuma gabashin Habasha.

  • Tun da farko shekarar 2011 ne kusan 'yan Somalia 15,000 suke tserewa daga kasar zuwa Kenya da Habasha a kowani wata domin neman abinci. Sansanin 'yan gudun hijira dake Dadaab a Kenya na dauke da kimanin mutane 370,000.

  • Manoma na fama da matsaloli da dama saboda tsadar abinci, abun da yasa suma suke tsere su bar dabbobinsu. 'Yawancinsu dai sun siyarda dabbobinsu saboda fari kuma wadanda suka rage suna ta mutuwa.

  • Da wuya dai a kawar da matsalar 'yan gudun hijira a yankin. Har wa yau mumunar rikici a yankin na kawo cikas ga shirye shiryen ci gaba a yankin, wanda kuma ka iya rage radadin farin da aka fama da shi.

  • Taimako wajen ayyukan ci gaba, zai yi tasiri ne wajen rage sassare itatuwa da kuma zaizaiyar kasa. Kuma sabbin ababen more rayuwa za su taimaka matuka wajen bunkassa ribar manoma a yankin

  • Sakamakon yanayi da rikici a yankin da kuma rashin sanya hannu jari a yankin, sama da mutane miliyan shida da dubu dari bakwai na Kenya kuma na fama da karancin abinci. Kungiyoyin bada agaji sunyi hasashen cewa mutane miliyan biyu da dubu dari shida na bukatar taimakon gaggawa a Somalia.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.