An sabunta: 11 ga Yuli, 2011 - An wallafa a 11:05 GMT

Hotuna: Bikin tunawa da Sheikh Nyass

  • Dubun dubatar musulmi mabiya darikar Tijjaniyya daga kasashen Afrika daban daban ne suka hallara a birnin Sakkwaton Najeiya domin bikin murnar zagayoyar ranar haihuwar jagoran darikar na yammacin Afrika Sheikh Ibrahim Nyass.
  • Bikin shine karo na dari da goma sha biyu da aka gudanar domin tunawa da Sheikh Ibrahim Nyass.
  • Darikar wadda Wani malami Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a shekarar 1784 a kasar Aljeriya tana daya daga cikin darikun addinin musulunci mafi yawan mabiya a yammacin Afrika da yankin Maghreb.
  • Mabiya darikar dai sun yi imani da yiwa waliyyai hidima a zaman watan samun kusanci ga Allah ta hanyar ceton waliyan.
  • Saboda cunkoson mutane a wurin taron, mutane da dama sun sume.
  • Ma'aikatan agaji, sun taimaka wurin daukan wadanda suka suma domin taimaka musu.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.