An sabunta: 13 ga Yuli, 2011 - An wallafa a 15:28 GMT

Hotuna: Matsalar fari a kusurwar Afrika

  • A karon farko an fara samun cikakkun bayanai game da girman yadda matsalar fari ke shafar kasashen dake kusurwar
  • Manyan kungiyoyin samar da agaji na Birtaniya na shirin fadada ayyukansu a kasar Somalia domin taimakawa wasu daga cikin mutane miliyan goma dake fuskantar barazanar yunwa a gabashin nahiyar Afrika.
  • Yankin dai na fama da matsanancin fari, sai dai kungiyoyin agaji sun rika fuskantar tarnaki sakamakon rashin tsaro a Somalia inda babu wata cikakakiyar gwamnati a shekaru ashirin da suka wuce.
  • Kwamitin kai dauki gagagawa na bala'oi ya ce Somalia na daya daga cikin wurare masu matukar wahala wurin samar da agaji.
  • Bugu da kari da dama daga cikin kungiyoyin samar da agaji na kasa da kasa an haramta masu aiki a wuraren dake karkashin ikon kungiyar islama ta al-shabab, da ake ganin tana da alaka da kungiyar alqaeda.
  • Sun galabaita sakamakon tsananin yunwa, ga kuma gajiyar tafiyar da suka yi ta kwana da kwanaki tare da yara kanananda ke fama da karancin abinci, inda suka hauro da su daga Somalia.
  • Kai kayan abinci zuwa sansanin Dolo Ado wanda ke wani kebantaccen wuri a yankin kudu maso gabashin kasar Habasha na da hadarin gaske, ga kuma nisa.
  • Kimanin motoci hamsin ne ke ratsa wannan hanya a ko wanne wata. Akwai bukatar kai kayan abinci daga Djibouti zuwa sansanonin dake kusa da iyakar kasar Kenya.
  • A makon da ya wuce ne kungiyar al-shabab tayi shellar cewa zata dage takunkunmi data sanyawa kungiyoyi samar da agaji na kasashen waje biyo bayan fari mai tsanani da ake fuskanta.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.