Farouk Mutallab zai kare kansa a kotu

Wata mai shari'a a Amurka ta yanke hukuncin cewa dan Najeriyar nan da ke fuskantar shari'a a kan zargin kokarin tayar da bam a cikin wani jirgin saman Amurka zai iya kare kansa da kansa.

A shekarar da ta wuce ne dai aka ce Umar Farouk Abdulmutalab ya sallami lauyoyin da aka shirya za su kare shi, inda ya ce zai iya kare kansa a wannan shari'a.

Ana dai yiwa shari'ar kallon ta na da wuyar sha'ani.

Tsarin shari'ar Amurkan dai ya baiwa mutumin da ake tuhuma damar iya kare kansa a kotu