An sabunta: 17 ga Oktoba, 2011 - An wallafa a 11:02 GMT

Hotuna: An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi

Hotuna: An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi

 • An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi
  Manyan motocin buldoza sun fara rushe Bab al-Aziziyya, tsohuwar fadar Kanal Gaddafi da ke birnin Tripoli na kasar Libya.
 • An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi
  Jami'an Majalisar rikon kwarya ta NTC sun ce za a maida wurin wani dandalin shakatawa na mutanen gari. A baya dai wuri ne mai sirri kuma jama'a na matukar tsoron kusantarsa.
 • An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi
  Har yanzu sojoji na ci gaba da tsare fadar. A 'yan kwanakin da suka wuce an samu harbe-harben bindiga tsakanin masu biyayya da kuma adawa da Kanal Gaddafi a birnin Tripoli.
 • An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi
  Dakarun Majalisar riko ta NTC sun rinka harba bindiga sama lokacin da manyan motocin ke rushe fadar.
 • An rushe tsohuwar fadar Kanal Gaddafi
  Kafin a kwace ginin ya sha fuskantar hare-haren bama-bamai daga sojojin kungiyar tsaro ta Nato.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.