An sabunta: 31 ga Oktoba, 2011 - An wallafa a 11:23 GMT

Dusar kankara ta mamaye wasu sassan Amurka

Dusar kankara ta mamaye wasu sassan Amurka

 • Dusar kankara a Amurka
  Miliyoyin Amurkawa daga garin Maine zuwa Maryland sun shafe karshen makon da ya gabata ba tare da wutar lantarki ba sakamakon karkarar da ke zuba a yankin Arewa maso gabashin Amurka, ciki harda birnin New York.
 • Dusar kankara a Amurka
  Hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi gargadin cewa za a fuskanci mummunan yanayi a kan titunan kasar.
 • Dusar kankara a Amurka
  Harkokin sufuri sun tsaya cak, inda aka soke tashin jirage da dama, sannan aka ayyana dokar tabaci a wasu biranen.
 • Dusar kankara a Amurka
  Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane tara saboda mummunan yanayin. Har ta birnin Washington ma bai tsira daga wannan yanayi ba.
 • Dusar kankara a Amurka
  A birnin Vermont na jihar New England wacce ta yi fice sakamakon kyawawan firannin da take da su, a yanzu dusar kankarar ta lullube firannin inda ta kara musu kyau.
 • Dusar kankara a Amurka
  Dusar kankarar da ke zuba dai ta haifar da tsaiko ga rayuwar jama'a ta yau da kullum a sassa daban-daban na Amurka.
 • Dusar kankara a Amurka
  Sai dai duk da haka kankarar bata hana jama'a zuwa kallon gasar NFL ba, inda dusar kankara ta mamaye wurin ajiye motoci a wasan New York Giants da Miami Dolphins a New Jersey.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.