An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 15:24 GMT

Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"

Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"

 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  Shekaru 12 bayan da yawan jama'ar duniya ya haura biliyan 6, Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kara taka wani muhimmin mataki.
 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  An bayyana jaririya Nargis daga birnin Lucknow na kasar India da cewa ita ce yarinya ta biliyan bakwai da aka haifa, a cewar kungiyar kare lafiyar yara ta Plan International.
 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  Kasashen Philippines ta bayyana Danica Camacho, da aka haifa a Manilla da cewa ita ce ta biliyan bakwai. Bangladesh da Cambodia na daga cikin kasashen Asia da suka ayyana na su yaran na biliyan bakwai.
 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  Shin ko wanne irin yara ne ake haifa da suka cike adadin na Biliyan bakwai. A tambayi Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon tambayar da yawancin mutane ke yi. Majalisar ta ce an yi kuskure wajen bayyana lokacin da za a haifi yaron na cikon biliyan bakwai, amma ta ce 31 ga watan Oktoba ita ce ranar da ta fi hasashe.
 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  A cewar majalisar, maimakon a rinka tambaya kan yawan mutanen, kamata ya yi a maida hankali kan ganin kowanne mutum ya kasance a raye cikin koshin lafiya.
 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  A lokacin da adadin jama'a zai fara raguwa a Asia, ana sa ran ya ci gaba da karuwa a nahiyar Afrika har zuwa wasu shekaru masu yawa.
 • Yaran da "suka cika adadin duniya biliyan 7"
  Kula da lafiyar jarirai da kuma iyayensu mata na da girman gaske a sassa daban-daban na duniya. Sai dai duk da wahala da kuma hadarin da ke tattare da haihuwar ga iyaye mata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce muyi murnar karuwar shekarun da jama'a ke yi a duniya da raguwar mace-macen yara kanana.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.