An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 10:14 GMT

Hotuna: An fara kidaya kuri'u a Liberia

  • An fara kidaya kuri'a a zagaye na biyu na zaben Shugaban kasar Liberia.
  • Ana kidaya kuri'un ne cikin duhu da dan fitulu saboda rashin wutan lantarki.
  • Dan takarar 'yan adawa, Winston Tubman ya janye daga takara.
  • Ya yi ikirarin cewar zaben ba a yi shi cikin gaskiya da adalci ba.
  • A zagayen farko, Shugabar mai ci, Ellen Johnson-Sirleaf, na kan gaba da kashi kusan arba'in da hudu cikin dari.
  • Wani wakilin BBC a Monrovia babban birnin kasar, ya ce a wata rumfa daya a birnin, mutane takwas ne kawai suka jira su kada kuri'arsu, ba kamar daruruwa a watan da ya wuce ba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.