Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Uganda ta ciri tuta a yaki da AIDS a Afrika

A nahiyar Africa kasar Uganda na daga cikin kasashen da ta zama wani babban abun misali a yaki da cutar AIDS mai karya garkuwa jiki.

A 'yan shekarun baya adadin wadanda ke dauke da kwayar cutar a kasar Uganda ya kai kashi goma sha takwas cikin dari, amma saboda matakan da gwamnatin kasar ta dauka, a yanzu haka mutanen da suke dauke da ita basu wuce kashi biyar cikin dari ba an al'ummar kasar.

Alhaji Musa Ahmed Bungudu, shi ne shugaban kula da aikace-aikacen hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a Uganda, wadanda suka hada da hukumar yaki da cutar ta AIDS.

A lokacin da ya kawo mana ziyara ofishinmu na London, Mansur Liman ya tambaye shi, ko menene aka yi a Ugandar da har ta zama abun misali?