Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Boko Haram sun shammace mu - Ministan Tsaron Najeriya

Matsalar tsaro na daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar shugabanni a Nigeria.

Ana cigaba da samun tashin bama-bamai da wasu nau'o'in ringingimu dake da nasaba da kabilanci da addini.

Wannana matsala dai ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyi a wasu jihohin kasar.

Sai dai kuma a nasu bangaren, mahukunta kasar sun ce suna iya kokarinsu don magance matsalar.

Aliyu Abdullahi Tanko ya tattauna da Ministan tsaron Najeriya Dr Bello Halliru Mohammed, inda ya soma bayani akan damuwar da gwamnati ke da ita kan tabarbarewar tsaro a kasar: