BBC navigation

Bikin baje kolin jiragen sama na Dubai

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 14:37 GMT
  • Mayan manyan kamfanoni kera jiragen sama, wadanda su ka hada da Airbus da Boeing sun hallara a bikin wasan jiragen sama na Dubai.
  • Sama da kamfanoni dubu daya ne daga kasashe hamsin ne su ka halarci bikin domin baje koli, wanda ake yi a kowacce shekara biyu.
  • A yanzu haka kowani daya cikin mutane biyar da su ka ziyarci Dubai sun fito ne daga wajen gabas ta tsakiya.
  • A bana sama da kashi talatin da biyar na masu baje koli a bikin sun fito ne daga hadadiyar daular larabawa. A shekarar 1989 kashi biyar ne kawai su ka fito daga kasar.
  • A bana sama da kashi talatin da biyar na masu baje koli a bikin sun fito ne daga hadadiyar daular larabawa. A shekarar 1989 kashi biyar ne kawai su ka fito daga kasar.
  • Akwai sabbin kamfanonin jiragen sama a hadadiyar daular larabawa da ma wadanda ke makwabtaka da ita.
  • Makwabciyar Dubai wato Abu Dhabi ta fara sarrafa kayyakin jirgi.
  • Hadadiyar daular larabawa dai na son zama cibiyar fasaha da kuma sarrafa kayyayaki.
  • Kamfanoni jiragen sama na amfani a duniya ne gabaki daya ba tare da la'akari game da inda su ka fito ba.
  • Kamfanoni jiragen sama dai ba sa fuskantar barazana duk da cewa dai ana fuskantar matsalar tattalin arziki a kasashen duniya.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.