Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Yadda shirin ya amfane ku

Shirin Haifi ki yaye dai shiri ne dake wayar da kan al'umma game da mahimmancin lafiyar uwa da ta yaro, musamman game da yadda ya kamata a kula da lafiyar mata a lokacin da suke dauke da juna biyu, ya zuwa haihuwa da rainon yaro.

Shirin ya tabo mahimman abubuwa da ya kamata uwa ta sani game da lafiyar kanta a lokacin da take da juna biyu, da yadda za ta raini cikin har zuwa lokacin da zata haihu, sannan kuma da irin kulawar da zata baiwa jaririn har ya girma.

Shirin ba wai akan mata kadai ya tsaya ba, ya duba irin gudunmawar da ya kamata mai gida ya baiwa uwargida a lokacin da take da juna biyu, ko lokacin haihuwa, tare kuma da taimakawa wajen kula da lafiyar uwa da ta yaron da aka haifa musamman ta bangaren taimaka musu da cin wasu nau'o'in abinci masu gina jiki ko kuma dawainiyar zuwa asibiti da kuma kara wayar da kan uwargida akan wasu abubuwa da ya kamata ta sani, wanda bata sani din ba da shirin ya tattauna akai.

A kan haka ne Wakiliyar BBC a Maiduguri, Bilkisu Babangida ta zanta da wasu domin jin irin yadda shirin na Haifi ki yaye da BBC Hausa ya wayar musu da kai sannan kuma a jihar Sokoto ma, wakilin BBC a can Haruna Shehu Tangaza ya jiyo mana ra'ayoyin wasu daga cikin wadanda suka saurari shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa da kuma yadda suka karu da shirin.

A yi sauraro lafiya