Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dan uwa rabin jiki

Hakkin mallakar hoto spl

A cikin filin Taba Kidi Taba Karatu na wannan makon, za ku ji labarin wadansu 'yan uwan juna su uku wadanda ciwon zuciya ya kama su a lokaci guda.

Biyu daga cikinsu dai, Guido, dan shekara 45, da Alberto, dan shekara 53, sun tafi yawan shakatawa ne a wani tsibiri a yankin Sicili na kasar Italiya da iyalansu sai ciwon zuciya ya kama Guido. Alberto ya rugo don ya kawo masa sai nan take shi ma ciwon zuciyan ya kama shi; nan take dai su biyun suka mutu.

Shi kuwa na ukun Salvatore, ya je duba mahaifiyarsu a asibiti, kusan a daidai wannan lokacin, shi ma a nan ciwon zuciya ya kama shi; sai dai likitoci sun ce shi ya yi sa'a saboda yana asibiti an yi nasara ceto rayuwarsa.