Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Muradun karni a Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yunwa, wani babban kalubale ne ga Afrika

Kasashen Afrika suna cigaba da yunkurinsu na cimma muradun karni na cigaba da Majalisar Dinkin Duniya ta tsaida nan da shekara ta 2015.

Bayanai daga kungiyoyin daban daban na Majalisar na nuna cewa Afrika na jan kafa wajen cimma wadannan muradu, idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi, kamar Asiya da kudancin Amurka.

A kan haka ne, gwamnatin Birtaniya ta shirya wani taron 'yan majalisun dokoki na kasashen kungiyar Commowealth a nan London, domin tattaunawa a kan irin cigaba da irin matsalolin da ake samu wajen cimma muradun na karni.

Horonrable Alhassan Ado Doguwa, shi ne shugaban kwamitin kula da muradun karni a majalisar Wakilan Najeria, har illa yau kuma shugaban Kwamitin Tarayyar Majalisun kasashen Afrika a kan batun na muradun karnin. Ya kuma yiwa Elhadji Diori Coulibaly karin bayani akan taron nasu.