Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki Yaye da BBC Hausa: Waiwaye adon tafiya II

Wani rahoto wanda hukumar abinci ta duniya, wato WFP, ta buga a watan Satumban shekarar 2010 ya nuna cewa mutane miliyan 925 ne ke fama da rashin isashshen abinci mai gina jiki a duniya a shekarar 2009.

Haka kuma kashi 98 cikin dari na wadannan al'umma na zaune ne a kasashe masu tasowa, inda kashi biyu bisa uku wato kashi 65 cikin dari ke zaune a kasashen Bangladash, da China, da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, da Habasha, da India, da Indonesia, da kuma Pakistan.

A ci gaba da waiwayen batutuwan da muka duba a baya, shirin Haifi ki Yaye da BBC Hausa na yau zai tabo batun abinci mai gina jiki da kuma bari da haihuwar bakwaini.

A yi sauraro lafiya.