Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Cikakken bayani kan cutar Noma

Image caption Wasu ma'aikatan asibiti

A cikin shirin na wannan makon za ku ji cikakken bayani a kan cutar Noma da ke zaizaiyar baki. Cutar dai tana kama yara ne masu shekaru 2 zuwa 6.

Galibi dai rashin tsaftar baki ne ke janyo cutar ta Noma, wadda ke fara kama dasashi , daga nan kuma sai kwayoyin cutar su samu shiga, har ciwon ya habaka, ya shafi duka bangaren fuska.

Dr Bashir Abduklkahi Jabo, shugaban Asibitin kula da masu cutar zaizayyar baki dake Sokoto, shi ne ya yi wa wakilinmu na Sokoto, Haruna Shehu Tangaza karin bayani a kan cutar ta Noma.